Saturday, 12 August 2017

Abin da Buhari ke bukata daga kafafen yada labaran Najeriya

Fadar shugaban kasa ta ba kafafen yada labarai tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bazata taba sa takunkumi a gare su ba.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adeshina ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, 10 ga watan Agusta a yayinda yake jawabi gurin taron shugabannin masu kafafen labarai na yanar gizo, a jihar Lagas.

A cewarsa gwamnatin shugaba Buhari na nan a kan bakarta na ba ‘yan jaridu da kafafen yada labarai yancin su, saboda haka babu ruwan ta da tunanin kafa wa kafafen yada labarai takunkumi.

Sai dai kuma ya yi nuni da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na son ganin kafafen yada labarai na tafiya a kan tsarin da ya kamata tare da kiyaye ka’idojin aiki ta hanyar yin sukar da ta dace, ba wai kowane kwaram da hama ya rika yayata kage, son rai da batutuwan da ka iya haddasa fitintinu ba.

Kakakin na Shugaban Kasa ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa, tun farkon kafa wannan kungiya, shi mamba ne a cikin ta, ya na mai karawa da cewa mambobin kungiyar mutane ne masu kima da mutunci a fannin aikin jarida.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: