Monday, 14 August 2017

Dalilai Goma (10) Dayasa Ake Son Rahama Sadau Fiye Da Kowace Jarumar Kannywood

Masoyan Rahama Sadau a shafin Suna na Instagram @Masoyan_rahama_sadau sun Rubuta Dalilai 10 da Suka sa jaruma Rahama Sadau Tafi Kowace Jaruma Masoya Wanda shafin Arewarmu.com yaci Karo dasu a jiya Lahadi.


Ga Dalilan Kamar Haka:

1. DALILI NA FARKO: @rahamasadau macce wadda bata wasa awajen sana'arta shiyassa kowa ne director yana shawar yayi film da ita SBD biyan Bukata, sannan Rahama Sadau musulma ce, shiyassa xakuga mafiyawanci masoyan musulmai ne.

2. DALILI NA BIYU: Rahama Sadau tana da mahassada da wa'yanda suka nuna kansu da ma wa'yanda suka boye Kansu, hakan ne ya sa a kullum take cigaba. Dama duk mutumin da yake rayuwa a doron kasa dole ne ya samu masu mishi hassada.

3. DALILI NA UKU: Rahama Sadau jaruma ce wacce take fitowa a kowani fanni, ko wani salo, babu irin salon da bazata fito maka a fim ba. Shi yasa kullum take kara haskakawa.

4. DALILI NA HUDU: Rahama Sadau jaruma ce wacce bata da girman kai, tayi daban da sauran matan masana'antar Hausa Film. Shi yasa tafi kowace jaruma masoya a Kannywood.

5. DALILI NA BIYAR: Rahama Sadau tana matukar kaunar masoyan ta, tana iya kokarin ta wajen faranta musu rai. Shi yasa a kullum masoyan ta suke Qaruwa.

6. DALILI NA SHIDA: Rahama Sadau tana da ilimin Addini da na Boko dai-dai gwargwado kuma tana aiki dashi yadda ya kamata.

7. DALILI NA BAKWAI: Rahama Sadau jaruma ce wacce ta fito daga wajen Sarki "ALI NUHU" wacce ta fito da kafar dama, Ali Nuhu mutun ne wanda bayi da wani buri wanda yawuci ya fito da Jaruma ko Jarumi har Allah ya daukaka su suyi suna.

8. DALILI NA TAKWAS: Rahama Sadau mace ce wanda ba ta son raini, bata shiga tsabgar kowa indai ba aiki ne ya hadasu ba. Idan ka ga ansamu matsala da ita to annemi aci mutuncin ta ne.

9. DALILI NA TARA: Rahama Sadau mace ce wacce take girmama na gaba da ita, idan har ta ga ka girme ta to zata yi iya kokarin ta wajen baka girman da Allah ya baka.

10. DALILI NA GOMA: Rahama Sadau tana matukar burge mutane tun lokacin da ta fara fitowa a fim din ta mai suna "GANI GA WANE" tun daga lokacin Mutane kesonta ba wata jaruma da ke burge mutane kamar ita.

Wadannan sune dalilan da ya sa Rahama Sadau a kullum masoyan ke mata addu'ar Allah ya rabata da sharrin masu sharri da sharrin mahasada da yayan BANZA.

Ku cigaba Da ziyartar Arewarmu.com Domin Samun Muhimman Abubuwa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: