Thursday, 10 August 2017

Hotuna: Yan Makarantar Firamari Masu Karatu Tsamo Tsamo A Cikin Ruwa

An gano wata makarantar Firamari a jihar Jigawa inda wasu dalibai kanana dake karatu a makarantar basu karaya ba, suke zuwa daukan darasi duk da malale makarantar da ruwan sama yayi.
Jaridar Rariya ta ruwaito an samu wannan makarantar Firamari ne a garin Marke, wanda ke cikin karamar hukumar Kaugama na jihar Jigawa.

A baya ma Arewarmu.com ra ruwaito wata makarantar Firamari a jihar Zamfara, wanda wasu mutanen kauyen garin tsafe suka gina da hannunsu, ginin kasa domin sama ma yayansu ilimin zamani.

Hakazalika sau dayawa, ana samun lalacewar makarantun ilimi, musamman a matakin Firamari, wanda shine tushen ilimi ga duk wani dalibi.


Da wannan muke ganin ya kamata hukumomin da abin ya shafa dasu jajirce wajen ganin sun baiwa makarantun Firamari kulawa ingantacce domin samar da ilimi sahihi.

Ga sauran hotunan yaran:

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: