Wednesday, 9 August 2017

Illoli 5 da kwanciya bisa katifa maras kyau ke haifarwa a jikin dan adam

Binciken masana harkar lafiyar dan adam a duniya sun yi bincike game da matsalolin dake tattare da kwanciya a kan katifar da bata inganci a jikin dan adam.

Dakta Ikechuku Amadi dake zaman wani babban likita a asibitin Abuja ne dai ya sanar da majiyar mu hakan yayin da kuma ya gargadi mutanen Najeriya da su kiyayi anfani da katifu marasa inganci.
Arewarmu.com ta samu cewa likitan ya kuma bayyana rashin samun isashiyyar barci wanda rashin shi kan iya jefa mutum cikin wani mawuyacin hali kamar su damuwa, tabuwar hankali da sauran su a matsayin wata babbar illa da rashin kyawun katifun keyi.

Haka ma dai kuma ya kara da wasu illolin kamar haka:

1. Ciwon baya.

2. Rashin samun isashshen barci.

3. Yawan yin minshari.

4. Rage karfin garkuwan jiki.

5. Yawan mantuwa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: