Monday, 14 August 2017

Tashin Hankali: Yadda Yan Fashi Sukayi Fashi A Masllacin Katsina

Wasu ‘yan fashi da makami guda 7 sun shiga hannun ‘yan sanda bayan da suka kaiwa wani dan kasuwa mai suna Alhaji Hassan Ishaku farmaki a wani masallaci da ke yankin Rafindadi a jahar Katsina.


‘Yan fashin sun isa masallacin ne dauke da wukake da addunan suka kwace kayayyakin kimanin N43,000 daga wajen Alhajin.

A karshen makon da ya gabata, ‘yan sandan suka gurfanar da su a kotun majistare da ke jahar, inda suka ce abunda suka aikata ya sabawa sashe na 96(2),(a) da 306 na kundin Dokar ‘Penal Code’ da dokar fashi da rike makamai.

‘Yan fashin sun hada da: Aliyu Arab, wanda aka fi sani da kolo; Amadu Suleiman, wanda aka fi sani da Jimmy; Murtala Ghali, wanda aka fi sani da Nasara; Hassan Lawal, wanda aka fi sani da Rugged; sai Ibrahim Haruna, wanda ak fi sani da Baba Iro.

Sai sauran, Bishir Ishak, wanda aka fi sani da Tinkiya; da Muntari Saidu, wanda aka fi sani da Maisalati.

Dukkaninsu mazauna yankin Mobil Rafindadi Quarters ne a Katsina.

Yanzu haka kotu ta bada umarnin a tsare su a gidan yari har ranar 23 ga watan Agusta yayin da za a saurari karar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: