Thursday, 30 August 2018

Amfani 5 Na ‘Ya’Yan Bagaruwa A Jikin Dan Adam

Bagaruwa, itacenta, ganyenta da ‘ya’yanta duka maganine kuma ana samunta a kasashe da dama kamar su india, austaralia, Da kuma kasashen Larabawa sannan an fi samunta a busashshen wuri.
Bagaruwa tana saurin saukar da masassara da kuma tsayar da zubar jini ko wane iri kuma ana amfani da ita wajen yiwa dabbobi magani. Ana amfani da bagaruwa wajen magance matsalolin fata, tsutsar ciki, tana karawa hakora karfi da haske kuma tana maganin ciwon hakora, sannan ana amfani da ita wajen magance matsalar ciwon suga, haka tana saurin saukar da gudawa.

A binciken da Dakta Bikram Chauhan ya yi a India a shekarar 1999, ya gano tana maganin hepatitis C birus.

Yadda Za A Yi Amfani Da Ita:

1.Ga Konewa, Toyewa Ko Kuma Gogewa: Ana daka ‘ya’yan bagaruwa a rika zubawa ko kuma a samu ‘ya’yanta wanda ba su bushe ba a rika matsa ruwanta a cikin wurin

2.Ciwon Hakori, Haskensu Ko Kuma Warin Baki: Ana samun iccen bagaruwa a yi asawaki da shi kullum in za a kwanta bacci haka idan aka tashi daga bacci. Ko kuma a samu itacenta a hada ta da jar kanwa a rinka kuskure baki da shi duk idan za a kwanta da kuma idan an tashi bacci.

3.Lafiyar Mata: A hada ‘ya’yan bagaruwa da itacenta da rihatul-hulbi a sa a wuta idan suka tafasa sai a sauke a tace a samu buta a zuba a rika tsarki da shi bayan minti 10 sai a sake sarki wannan yana matse macce kuma yana maganin toilet Infection sannan yana saka ta kamshi sosai.

4.Matsalar idanu: A samu ganyen bagaruwa a tafasa, idan ya tafasu a juye a buta a rika wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido in sha Allahu.

5.Amfanin ta ga Maza: Duk wanda ke saurin biyan bukata kafin matarsa zai iya amfani da ‘ya’yan bagaruwa ya daka ta sai ya zuba ruwa ya rinka sha In sha Allahu zai ga canji. Godiya ga Allah (SWT) da ya saukar mana da bagaruwa da sauran abubuwa na yau da kullum. Allah ya kara mana Lafiya, amin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: