Thursday, 30 August 2018

Amsoshin Tambayoyinku: Menene Hukuncin Mijin Da Ke Yiwa Matarsa Istimna’i ?

TAMBAYA
*******************
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu

Allah ya taimaki Malam, Malam Ina tambaayane illolin Istimnai?

2.Menene hukuncin mijin da baya iya biyawa matarsa bukatarta da Al aurarsa saida yatsa ,shin hakan za’a kirashi Istimnai ne? Amma hakan da baya faruwa Sai da yaqara aure sai ya zamana al-aurarsa baya motsawa a gurin uwargida. Shin ya halasta ta nemi saki? Don tanata hakuri amma har yanzu ba Chanji. Allah ya bada ikon amsawa.

Daga dalibarku ta zauren Fiqhu.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ya halatta Miji yayi wasa da matarsa ta kowanne yanayi, Mutukar hakan bai sa’ba da shari’ah ba, Kuma mutukar ba zai chutar da lafiyarta ba.

Haramtaccen istimna’i shine wanda mutum yayi ma kansa. Amma ya halasta Miji yayi ma matarsa, ko kuma ita matar tayi ma Mijinta.

Amma idan ya zamanto miji ya kasa biyan bukatar Matarsa sai ta hanyar sanya yatsa ko wani abu agabanta, Kuma hakan yana chutar da lafiyarta, Kuma ba ya gamsar da ita, to rashin yin yafi alkhairi.

Tunda har ya zamanto ba ya iya kusantarta ma gaba daya, ya kamata su kira magabatansu suyi zama, abashi lokacin da zai nemi magani. Idan ya warke shikenan. Amma idan bai samu magani ba sai araba auren don gudun chutarwa ga lafiyarta da imaninta da tarbiyyarta.

Allah yace “IDAN KUNJI TSORON CHUTARWA ATSAKANINSU TO KU SANYA MASU YIN HUKUNCI DAGA MUTANENSA DA MASU YIN HUKUNCI DAGA MUTANENTA IDAN SUN NUFI YIN SULHU TO ALLAH ZAI DATAR DA TSAKANINSU”.

Istimna’in da mutum ke yiwa kansa yana da illoli masu yawa da yake haifar wa jikin Dan Adam. Misali kamar ciwon kai, rashin nutsuwa, rikicewar tunani, rashin karfin jiki, raunin jijiyoyin al’aura, ciwon baya, rashin karfin idanu, etc.

To amma koda irin wannan da ma’aurata ke yiwa junansu idan yayi yawa zai iya haifar da wadannan matsalolin ko fiye da haka.. Don haka ya zama wajibi akiyaye kada amayar dashi abun yau da kullum.

WALLAHU A’ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (02/08/2018 20/11/1439).

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: