Monday, 13 August 2018

Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Wasu malaman addinin musulunci a arewacin Najeriya a ranar Lahadi sun yi wani taro a garin Kaduna inda suka koka tare da yin tir da mabiya tafarkin shi'a almajiran Zakzaky watau Islamic Movement in Nigeria (IMN).
Malaman dai sun yi taro ne na kaddamar da wani littafin da shehin malami Farfesa Umar Labdo na jami'ar Maitama Sule dake garin Kano ya rubuta game da akidun shi'a da kuma dabi'o'in su da ya bayyana a matsayin marasa kyau kuma abun kyama.


Mun samu cewa shima babban sakataren kungiyar Jama'atunnasrul Islam Dakta Khalid Aliyu Abubakar ya bayyana kungiyar a matsayin abun kyama sannan kuma ya bukaci hadin kan jama'a domin ganin an kawo karshen ta.

Daga karshe dai malaman sun yi ittifakin cewa da ilimi ne ta kuma hanyar wayar ma da al'umma kai da irin litattafai makamantan wadan nan ne za a iya kawo karshen na shi'a a yankin na arewa

A wani labarin kuma da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa an ga gawar daya daga cikin hadiman Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano kuma mai taimaka masa na musamman mai suna Mista Randie Chima a dakin sa.

Majiyar ta mu dai ta tabbatar mana da cewa a ranar Juma'a hadimin gwaman yayi ta hidimar sa lafiya lau kuma har ma yaje wani wurin shagali da daren juma'ar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: