Monday, 13 August 2018

Yadda na kubuta daga masu safarar mutane zuwa kasar Saudiyya, bayan dandana azaba da na yi

Shugaban Hukumar hana safarar mutane ta Kasa NAPTIP, Julie Okah–Donli ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin Najeriya za ta dawo da wasu mata 50 da ta ceto daga kasar saudi Arabia, suna aikin Bauta.

Donli ta bayyana cewa hakan ya yiwune bayan kwamiti da ministan Harkokin Kasashen waje Geoffrey Onyeama ya kafa domin binciken wadanna korafe-korafe da nemo hanyoyin da za a bi a dakile ayyukan masu safarar yara mata zuwa kasar Saudi Arabiya,
” Mun tafi kasar Saudi Arabiya domin gani wa idanun mu abubuwan dake faruwa a can musammam ga matan da akayi safarar su da sunanan sama musu aiki. Ko da yake tun kafin nan wasu na kiran mu daga kasar suna neman a kawo musu dauki a dalilin halin da suka shiga tun bayan tafiyar su kasar.
” Da yawa daga cikin su sun makale a kasar babu yadda za suyi su dawo Najeriya ma.”
Minista Onyeama ya jinjina wa kokarin NAPTIP, yana mai cewa gwamnati ba za ta zuba ido ta bari wasu na yin safarar mutanen Kasar nan zuwa kasashen waje ba sannan suna fakewa da wai aiki suke nema musu.
” Matasa ne suka fi fadawa cikin wannan matsala, domin kuwa a yanzu bayan irin bayannan da muka samu game da irin wahalhalun da suke sha idan aka tafi da su can kasar, wasun su ma basa iya dawo wa.
” A haka dole ne ya sa gwamnati ta sake bude sabuwar faifai domin ganin ta dakile duk shirin da masu rin wannan aiki na safara rmutane bai yi nasara ba.
Ya kara da cewa gwamnati zata duba yadda ake amfani da iyakokin kasar nan don aikata irin wannan aiki da ganin an kawo karshen sa.
YADDA AKA TAFI DANI KASAR SAUDIYYA
Wata daga cikin wadanda aka ceto daga kasar ta bayyan yadda ta fada tarkon masu yin safarar mutane har ta sami kanta a kasar Saudiyya.
” Wata kawata ce ta hada ni da wata mata da ga dukkan alamu ejen ne irin masu shiryawa da nemo mutane domin safar su zuwa kasashen waje. Ita kanta kawata din ce mini ta yi wai tana zama ne a Dubai.
” Daga nan sai ta umarceni da in zo Abuja domin mu hadu da matan, domin ni a Legas nike zama.
” Bayan mun hadu sai aka kaini wani Asibiti a ka yi mini gwaje-gwaje. Daga nan sai matan tace mini za a kai ni kasar Saudiyya domin yin aiki. Ta ce min za a dinga biya na naira 150,000 duk wata.
” Aka yi mini takardun tafiya. Muna isa kasar Saudiyya sai komai ya canza. Na kare ne dai a akin wanke-wanke da shara, sannan suka kwace mini fasfo di na.
” Da wahalar ta yi yawa sai na kira ejen din, na gaya mata halin da nake ciki. Sai tace dole fa sai na ci gaba da zama a wannan wuri da nake aiki domin sai na yi aikin Naira Miliyan 1.7 tukuna kafin in bar gidan. Idan ba haka ba kuwa sai fa nayi aikin shekara biyu kafin a dawo dani gida.
” A haka ne fa na samu na kira wani abokina dan jarida shi kuma ya taimaka mini ya hada ni da NAPTIP, su kuma suka tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Saudiyya har Allah yayi na kubuta daga hannun wadannan mutane.
Ta roki gwamnati da ta karkato akalar ta zuwa kasar Saudiyya domin kuwa akwai dubban matasa ‘yan Najeriya da aka yi safarar su zuwa kasar suna aikin bauta a can.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: