Thursday, 30 August 2018

Yadda Za Ki Yi Amfani Da Fiya (Avocado Pear) Wajen Gyran Jiki Da Fatar Fuska

FIYA: Wata dan itaciya ce mai kunshe da sinadarai da suke taimakawa wajen gyaran fata tare da kara inganta ta, ba tare da an kasha kudi mai yawa ba, kuma cikin sauki.

Fiya na kunshe da sinadarin bitamin c wanda yake kare fata daga fesowar kurajan fuska, da hana ta tamushewa, musamman in zaki juri cin fiya a kullum. Bayan ga wannan sinadarin, fiya na kunshe da sinadarin bitamin E da Carotin wandanda suke kare fata daga illolin hasken rana. Sinadaran da ke cikin basu tsaya a nan ba, fiya na kunshe da sinadarin “oleic acid” wanda yake taimakawa fata wajen sanya ta tayi laushi da kuma kare ta daga bushewa. ‘Yar uwa cin fiya a kullum na da tasiri da amfani ga lafiyar fata da kuma jiki.

ABUBUWAN DA ZAKI BUKATA IN ZA KI KWABA FIYA (FOR FACE MASK)

*Fiya (Avocado pears)

*Lemun tsami (Lemon)

*’Danyan Kwai (Egg)


Da farko ‘yar uwa za ki samu fiyar ki mai kyau, sai ki bare ta, sannan ki yayyanka ta, ki zuba a injin nika (blender) ki markada, sannan ki juye shi a kwano mai tsafta, ki dauko dayan kwai sai ki fasa daya akai, sannan ki kada wannan kwabin har sai ya zama daya.

In kin kasance mai kuraje a fuska sai ki dauko Lemun tsamin ki, ki matsa a kan wannan kwabin. Bayan kin wanke fuska da ruwa da sabulu, in kika tsane fuskarki sai ki dauko wannan kwabin ki shafe fuskar da shi, bayan minti 20- 30 sai ki wanke. Za ki iya yin haka sau biyu a sati.

A binda za ki kula anan shi ne, sanya Lemun tsami a kwabin yana hana fitowar kuraje da rage maikon fuska. ‘Yar uwar, muddin za ki jure yi sau biyu a sati fuskarki za ta na sheki, haske da kyan gani. Kin san an ce ko kana da kyau to ka kara da wanka. Allah ya sa mu dace.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: