Buhari ya fidda dala biliyan 1 don gudanar da wasu muhimman ayyuka 3 a kudu 2 a Arewa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin ware naira biliyan daya, kimanin naira biliyan dari huru da sittin da takwas kenan (N468bn) don aiwatar da wasu muhimman ayyukan cigaban kasa a Najeriya.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito ministan watsa labaru, Alhaji Lai Muhammed ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba a yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Najeriya, NTA, inda yace za’a fidda wadannan kudade ne daga asusun hadakan gwamnatin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi, watau ‘Sovereign wealth fund’.
ministan ya zayyana ayyukan gida biyar kamar haka;
Aikin titin Legas zuwa Ibadan
Aikin gadar Neja ta biyu
Aikin babbar hanyar data hada yankin Inyamurai da na kudu maso kudu
Aikin layin dogo daga Abuja zuwa Kano
Aikin wutar Mamabilla.
Minista Lai yace gwamnatin Najeriya ya mayar da hankali wajen samar da manyan ayyukan cigaba, kuma zata cigaba da tayar da duk wani aiki da gwamnatocin baya suka yi watsi dasu don ganin ta kammala su a cikin wa’adinta.
“Muna ganin gwara mu cigaba da tsofaffin ayyuka tare da kammalasu gaba daya, kafin mu fara sabbin ayyuka, saboda haka ne a shekarar 2017 aka ware naira biliyan 14 107 akan ayyukan sufuri, biliyan 130 akan harkokin noma da samar da ruwan sha, da kuma naira biliyan 325 akan harkokin wuta, manyan ayyuka da gidaje.” Inji shi.
Lai yacigaba da fadin “Daga shekarar 2016 zuwa 2017, mun kashe naira triliyan 2.7 akan manyan ayyuka, ba’a taba samun irin haka ba a tarihin Najeriya gaba daya.”
Daga karshe ministan ya bayyana ayyukan titin Oyo zuwa Ogbomoso da kuma aikin kilomita 240 na titunan gwamnatin tarayya dake garin Fatakwal a matsayin ayyukan da gwamnati ke yi da kudaden da ta ciyo bashi daga bankin musulunci ta Duniya.
0 comments: