Sunday, 16 September 2018

Rashin adalci: Wasu 'yan Najeriya sun yo ca akan Buhari game da sabbin nade-naden sa

Wasu 'yan Najeriya musamman ma daga bangaren kudancin kasar nan sun yi ta surutai da gungunai ga Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari game da sabbin nade-naden da ya yi a 'yan kwanakin nan.


Yan Najeriyar dai wadan da suka nuna rashin jin dadin su musamman ma a kafofin sadarwar zamani, sun bayyana nade-naden a matsayin babban rashin adalci da kuma tsantsar son kai daga bangaren na shugaban kasar da suka zarga da nada 'yan arewa kadai.

Mun samu labari cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne shigaban kasar ya nada Yusuf Bichi wanda dan asalin jihar Kano ne a matsayin shugaban hukumar jami'an tsaron farin kaya na DSS.

A jiya kuma shugaban ya nada karamar ministar kudi da ta fito daga jihar Sokoto a matsayin babbar ministar kudin ta wucin gadi biyo bayan murabus din Kemi Adeosun.

A nasu bangaren, suma dai wasu 'yan arewar da dama sun nuna goyon bayan su ga shugaban kasar game da nade-naden inda suka ce ba laifi bane.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar shugaban kasar Najeriya a zabukan 2019 dake tafe mai suna Fela Durotoye, ya roki 'yan kasar da su taimaka masa su tattara masa kudin da zai sayi fom domin takarar tasa a jam'iyyar adawa ta Alliance for a New Nigeria (ANN).

Mun samu cewa fom din takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawar dai ana saida shi ne akan Naira miliyan 3.5 wanda ya bayar da shawarar cewa da an samu mutane kadan da kowa ya bayar da Naira dubu daya to za a hada masa kudaden fom din.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: