Sunday, 16 September 2018

Wani ‘Dan Najeriya da ya hana Turawa sakat da 419 ya shiga hannu

Mun samu labari daga BBC cewa an kama wani ‘Dan Najeriya da ya hana Turawa sakat da damfara. ‘Yan Sanda Kasar Australlia ne su ka cafke wannan hatsabibin mutumi da ya gagari jama’a.

Jami’an tsaron na kasar Australia sun yi nasarar damke ‘Dan Najeriyar da ke damfarar mutane ta hanyar aika wasu sakonni na bogi a shafukan zamani na gizo. Wannan mutumin Najeriyar shi ne shugaban masu wannan danyen aiki na 419.

Yanzu haka dai har wadannan ‘Yan damfara sun tara makudan kudin da su ka haura fam Miliyan 3 na Dalar kasar Australia. Wannan mutumi dai yana yin wannan aiki ne daga wata cibiyar tsaro a babban Birnin Sydney na kasar ta Australia.


Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda na kasar Arthur Katsogiannis ya bayyana cewa zai yi wahala a iya gano wadannan kudi domin tuni har an aika su Najeriya. An dai dace wajen cafke wasu daga cikin masu wannan mugun aiki a kasar.

Abin mamakin dai shi ne yadda ake damfarar mutane daga cikin cibiyar tsaron Hukumar shige-da-fice da ke Garin Villawood a cikin babban Birnin Sydney. Daga cikin wadanda aka kama har da wasu mata da kuma Matashi mai shekara 20.

BBC Haussa ta rahoto cewa an yi kira ga kamfanoni su rika lura da shafukansu na yanar gizo tare da inganta tsaro da kuma bi a hankali da kudin shiga. Masu wannan abu kan labe ne da soyayya wajen damfara ta hanyar zamba cikin aminci.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: