- Wani jami'in NSCDC a jihar Maiduguri ya harbe matsarsa, kanwarsa da wasu 'yan uwansa biyu
- Bayan harbe su, jami'in ya yi wurgi da bindigansa inda ya tafi ya sha guba shi ya ce ga garinku
- Yan sanda sun fara bincike domin gano abinda ya janyo mutumin ya aikata wannan abin mai tayar da hankali
Wani jami'in Hukumar Tsaro ta NSCDC a kashe kansa bayan ya harbe matarsa da kaninta da wasu mutane biyu a kusa da tashan mota na Borno Express a jiya Juma'a.
A cewar wani majiya daga hukumar 'yan sanda, " haka siddan mutumin ya harbe mutane hudu ciki har da matarsa da 'yan uwanta biyu da kuma kanwarsa. Matarsa da dan uwanta sun mutu nan take."
Wani majiyar kuma da ya taimaka wajen ceto rayukkan wadanda aka harba din ya tabbatar da cewar jami'in NSCDC din ya yi wurgi da bindigarsa ya tsere inda ya sha wani abu da ake kyautata zaton guba ce kafin wani ya tsince shi.
An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiuguri misalin 8.30. An bashi gado a asibitin amma ya rasu misalin karfe 9 na daren Juma'a.
Sauran mutane biyun da ya harba suna asibitin suna karbar magani.
Wani jami'in NSCDC a jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce abu ne mai tayar da hankali.
Ya kara da cewa jami'an 'yan sanda suna gudanar da bincike domin gano musababin abinda ya janyo afkuwar wannan lamarin.
Saturday, 27 October 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: