Harka ta lalace: Maciji ya makalewa wani mai wasa da shi a cikin baki a Najeriya
Daman dai Hausawa na cewa dukkan mai wasa da maciji to idan ba sa'a ba shine zai yi silar ajalin sa. Wasa da maciji dai ya zama tamkar ruwan dare a kasar Najeriya inda wasu kan dauki hakan tamkar sana'a da sukan yi domin su samu taro da sisi.
Za'a iya ganin irin mutanen nan a kasuwanni, bakin hanya ko kuma inda mutane kan taru suna wasa da macijin domin kayatar da masu tafiya ko kuma masu sha'awa da kan zo kallon su har ma kuma su basu wani abu.
Wasu kuma musamman ma masu saida magani irin na gargajiya kan yi anfani da macijin domin jan hankalin al'uma.
ta ci karo da wani faifan bidiyo na wani mai wasa da maciji a birnin Legas, tarayyar Najeriya da yake ta kokowa da wani macijin da ya saka a cikin bakin sa yana wasa da shi amma kuma yaki fitowa.
Mun dai ga bidiyon inda mutumin yake sanye da bakaken kaya yana ta kuma kokarin amayo da macijin daga cikin bakin sa amma ya ki amayuwa.
0 comments: