Thursday, 15 November 2018

MAHIMMANCIN ZABEN BUHARI A KARO NA BIYU GA YAN NAJERIYA.

MAHIMMANCIN ZABEN BUHARI A KARO NA BIYU GA YAN NAJERIYA.



Wajibi ne mu tashi mu tsaya akan kafar mu wajen fahimtar da Talakawan Najeriya mahimmancin zaben shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu, da kuma wayar da al'ummah rashin zaben shi a karo na biyu mai zai haifar na cibaya a kasar mu Najeriya.

Inaso mu fara da dubi da irin aiyukan cigaban kasa da gwamnatin Shi ta shinfida a doron kasar nan duk da cewa ba'a kammala wasu ba, yayi aiyukan ne cikin irin matsalolin da Sanatocin PDP da munafukan Sanatocin PDP da suka saka rigar APC a zaben 2015 suka jawo na jinkirta kasafin kudin kowace shekara cikin ukun da suka gabata karkashin Mulkin shugaba Muhammadu Buhari, da kawo cikas a abubuwan more rayuwa wanda suka ki amincewa da shi don kar aiyukan su amfanar da Talakawan Najeriya, amma cikin ikon Allah baba Buhari yayi abubuwan da zai kasance abin alfahari a yan Najeriya na har abada.

Da farko zan fara da bada shawara a yan Najeriya suyi amfani da daman da suka samu na zaben Shugabanni masu mulki da wakilai a shekarar 2019, su tsaftace Majalisar tarayya na wakilai da dattijai, su tura wakilan da zasu amince da duk wani udurin da shugaba Muhammadu Buhari yakai zauren majalisa domin anfanuwar Talakawan kasar da cigaban kasar.

Inaso Talakawan Najeriya su fahimci basu da matsalar daya wuce Yan Majalisar dattawa da wakilan kasar nan, ya zama wajibi mu tsaftace zauren majalisa a zaben 2019, mu tabbatar yan majilisun mu na wakilai da dattawa na karkashin Jam'iyyar Muhammadu Buhari sunyi rinjaye a majalisa, su nunka na jam'iyyar adawa da Buhari Uku ko fiye da haka.

Tsaftacce Majalisar shine zai bada dama a Gwamnati shugaba Muhammadu Buhari ta kawo gyara cikin al'amuran Gwamnati a karamin lokaci, sa'anan aiyukan da yake na alheri zai nunku akan na yanzu, shugaba Buhari ko a yanzu yayi aiyukan alherin da bazai irgu ba, musamman ma a bangaren shinfida hanyoyi kudanci, yammaci da arewacin kasar nan, samar da ingantaccen wutar lantarki, samar da tsaro da inganta tattalin arziki don Kasar ta dogara da kanta.
Yanzu haka akwai manyan mahimman aiyukan da Gwamnatin Buhari take a sansa daban-daban a fadin Kasar nan, kuma bata kammala su ba, rashin zaben shi zai haifar da tsayawar aiyukan domin shikadai ne mai kishin dazai iya cigaba da aiyukan.

Yan uwana yan Najeriya, mu farka daga barci, mu tsaya akan kafafun mu, 2019 damace agare mu, mu zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, mu tura masa wakilai yan jam'iyyar sa, kar mu zabe shi mu tura masa yan majilisun PDP wanda zasu shafe shekara 4 suna adawa da gwamnati shi da kawo cikas akan duk wani kuduri na aiyukan alherin da Gwamnati shi zatayi domin jin dadin rayuwar ku.
Amma ku sani ko kun zabe shi indai baku tura masa wakilai na jam'iyyar saba, akwai sauran runa a kaba, domin kuwa

"KWALLIYA BAZATA BIYA KUDIN SABULU B" har sai kun tura masa yan majilisun jam'iyyar sa ta APC sunyi rinjaye ninki 3 ko 4 yan jam'iyyar adawa da gwamnatin sa.
Zakuji ni a rubutu na gaba akan irin aiyukan alherin da Gwamnati shugaba Muhammadu Buhari tayi a fadin kasar nan.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: