cewa har yanzu ana gwabzawa tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a garin
Shugaban bayar da horo da ayyuka na soji, Manjo Janar Lamidi Adeosun ne ya bayarda wannan sanarwar a taron manema labarai da ya kira a hedkwatan Operation Lafiya Dole a Borno,
Wannan sanarwar ta hukumar sojin yana zuwa ne a lokacin da wasu rahotanni ke yaduwa na cewa mayakan kungiyar Boko Haram na sashin Albarnawi sun kwace garin Baga a jihar Borno,
A baya, an ruwaito cewa wani jami'in sojan ruwa ya rasa ransa yayin artabu da sojoji su kayi da 'yan ta'addan kungoyar Boko Haram a hedkwatar jami'an tsaron hadin gwiwa ta MNJTF a Baga na jihar Borno,
A ranar Laraba, hukumar sojin Najeriya ta ruwaito cewa dakarun sojin suna fafatawa da 'yan ta'adda a Baga sai dai ba a bayar da cikakken bayanin abinda ke faruwa ba,
A wata sanarwa da Brig. Janar Kukasheka Usman ya fitar a ranar Alhamis, ya ce dakarun sojin Najeriya ta takwarorinsu na sojin ruwa fafata da mayakan Boko Haram cikin daren Alhamis,
Mai magana da yawun sojin ya ce, dakarun soji na Operation 3 na Lafiya Dole suna cigaba da artabu da 'yan ta'addan.
Ya kuma ce jami'an sojojin sama sun fara yiwa mayakan na Boko Haram luguden wuta a yayin da suke kokarin tserewa.
0 comments: