Tuesday, 14 February 2017

Shirye Nake Mu Shirya da Kwankwaso – Inji Ganduje

Gwamna Ganduje na Jahar Kano ya bayyana cewa a shirye yake da ya shirya da Tsohon Gwamna Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya bayyana hakan ne bayan ya tabbatar da cewa akwai Baraka a tsakanin su.
Ya bayyanawa manema labarai cewa sunyi zaman mutunci da Kwankwaso kuma abokinsa ne na tsawon lokaci.
Rikicin nasu ya haifar da bangarori biyu Kwankwasiya da Gandujiya a Jam’iyar ta APC a Jahar Kano.

Duk da dai kwananan Gwamnan Katsina ya bayyana cewa suna iya kokarin su don ganin sun shawo kan wannan Matsalar domin Gwamnonin Arewa sun bayyana basu jin dadin irin abunda ke faruwa tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Amma dai shi gwamna Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake da ya shirya da Kwankwaso.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: