Friday, 31 March 2017

Rumbun Dariya: Muna Saya Mishi (Muntsaya Mata)

Wani Inyamiri ne ya halarci zaman kotu sai kuwa ya yi sa’a a ranar ana zaman sauraron karar wata mace da aikata zamba.

Da aka kammala sauraron karar sai Alkali ya yanke wa matar hukunci daurin shekaru biyar ko kuma tarar Naira dubu dari biyu da hamsin.
Sai Alkali ya yi tambaya da cewa za a tafi da matar gidan kaso amma idan har da akwai wanda zai tsaya mata, to fa za ta iya samun ‘yancinta.


Inyamiri ya dubu ya ga babu wanda ya mike ya ce zai tsaya wa matar nan, Sai ya ce a ransa “Hausa mugu ne walayi, zai bari wannan mutum ya yi cekala biyaru a prison saboda tsayawa”
Sai ya mike tsaye ya ce “Alkali, Mun saya mishi”
Sai Alkali ya ce to tunda an samu wanda zai tsaya mata ba za a kaita gidan kaso ba. Kai kuma ya ya sunanka? Alkali ya tambayi Inyamiri.
Inyamiri ya masa da sunanmu ne Chinedu.
Sai Alkali ya ce to, za ka biya tarar Naira dubu dari biyu da hamsin don wannan baiwar Allah ta samu ‘yancinta kamar yadda ka fada cewa ka tsaya mata.

Chinedu ya ce “Mene ne?”

Alkali ya ce Naira dubu dari biyu da hamsin
Chinedu ya ce ” Na two hundred and fifty thousand naira be that oo”

Alkali ya kwarai

Sai Chinedu ya ce “Oga Alkali, mun zauna mishi…kai munkwanta mishi”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: