Thursday, 30 March 2017

Idan Kaji Abinda Ke Cikin Lemon Coca-Cola Bazaka Kara Sha Ba (Karanta)

A wata kasa dai abin da aka samu cikin gwangwanin lemun nan na Coca-Cola ya ba Jama’a tsoro. Da dama dai ba za su kara sayen wannan lemu su sha ba.
Dama can dai ana ta kishin-kishin din cewa lemun nan da aka saba sha watau Coca-cola na da mugun illa har ta kai Gwamnatin tarayya tayi magana game da lafiyar lemun na Coca Cola. Ministan lafiya na Najeriya ne ya wanke masu lemun kwalban.

Sai dai a can wata kasa an samu najasa ne ma a cikin lemun hakan ta sa aka fara bincike game da Coca-Cola. An dai samu najasar mutum ne a cikin gwangwanin lemun da aka bude a kasar Ireland.

Ana zargi cewa kwalaben lemun sun shigo ne daga kasar Jamus wanda tuni Jami’an ‘Yan Sanda da sauran Ma’aikata su ka fara bincike game da yadda wannan abu ya faru. Coca-Cola dai ta maida martani kamar yadda mu ke samun labari a nan Arewarmu.com.

Haka ma dai kwanaki a Najeriya Misis Boade Akinola ta Ma’aikatar lafiya ta bayyanawa manema labarai cewa bincike da aka yi ya nuna cewa sinadarin da ake gudu na Benzoic acid da ke cikin lemun bai da wani yawan da har zai yi illa a jikin mutum.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment: