Wednesday, 3 October 2018

Al’ajabi: Wani Mutum Ya Kai Kanshi Ofishin ‘Yan Sanda Dauke Da Kan Abokinshi Da Ya Kashe

A wani lamari mai matukar daure kai, wani mutum mai shekaru 28 ya kai kanshi ofishin ‘yan sandan dauke da kan abokinshi da ya gille bayan ya kashe shi.
Mutumin mai suna Pashupathi dan yankin Mandya ne a garin Karnataka da ke kasar India.

Sufeton ‘yan sandan yankin, Shivaprakash Devaraj, ya fadawa manema labarai cewa Pashupathi ya kashe abokin nashi mai suna Girish a sakamakon wata ‘yar hatsaniya da ta hada su.

Pashupathi ya isa ofishin ‘yan sandan jikin shi duk jini a ranar Asabar da ta gabata, inda ya shaidawa musu cewa Girish ya zagi mahaifiyarshi, shi ya sa ya aikatar masa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: