Thursday, 16 August 2018

Musha Dariya: Ku Karanta Labarin Dan Fulani Da Sa

Wani dan fulani ne yakai saniyar shi kasuwa amma ba’a siya ba sai ya dawo gida ranshi a bace.

Sai matar shi ta tambaye shi meyasa yake fishi sai yace mata ai saniya ce nakai ta kasuwa amma ba’a siya ba sai matar tace ai kaine baka nemi shawarata ba gobe idan ka koma kasuwar kace saniyar tana da ciki.


Haka kuwa akayi dan fulani yakai saniya kasuwa yace tanada ciki nan danan aka siyeta tayi kudi fiye da kima kawai sai dan fulani yayi ta mamaki yadawo gida yana murna.

Rannan sai akazo neman auren Diyarshi sai aka kira liman ya yanke sadaki dubu 11,000 sai dan fulani yace dakata malam nifa diyata tana da ciki gara ku sani dan likita ma yace yan biyu zata haifa.

kunjifa gogan naku HAHAHAHAHAHA

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: