Thursday, 30 March 2017

Buhari Ya Fasa Komawa Kasar London, Karanta Dalili

A ranar Laraba 29 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza shawara dangane da duba lafiyarsa, inda fasa komawa kasar Ingila domin ganawa da likitocinsa.
Tun a ranar da shugaba Buhari ya dawo ne ya shaida ma yan Najeriya zai sake komawa kasar Ingilan don a cigaba da duba lafiyarsa, amma a yanzu shugaban ya canza shawara, inda ya gayyato likitocin nasa, kuma ana sa ran zasu hallara Najeriya a ranar Juma’a 31 ga watan Maris.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana ma Sahara Reporters cewar tun a ranar Laraba ne tawagar shugaban kasa suka fara tafiya kasar Ingila, inda suka bi jirgin Ethiopia, amma a yanzu haka an kira su daga fadar shugaban kasa cewa su dawo gida.

Majiyar ta shaida ma Sahara wasu jiga jigan jami’an fadar shugaban kasa ne suka bashi shawarar kada ya koma, bayan kwashe sati 7 a kasar waje, idan ba haka ba za’a cigaba da watsa jita jita da dama wanda ka iya shigar da kasar cikin rudani.

Cikin wani gajeren bayani da Buhari yayi a ranar daya dawo, shugaba Buhari ya shaida ma yan Najeriya cewa zai koma kasar Ingila don a cigaba da duba lafiyarsa nan bada dadewa ba. Sai dai sakamakon halin da siyasar kasar ta fada, shugaba Buhari ya fasa komawa.

Idan mai karatu bai manta ba Arewarmu.com ta dauko rahotom tafiye tafiyen da shugaba Buhari yayi zuwa kasar Ingila a baya domin duba lafiyarsa. don a watan Yulin shekarar 216 sai da shugaba Buhari yaje birnin Landan don a duba lafiyar kunnensa. Wannan lamari ya biyo bayan korafe korafe da wasu kungiyoyin kare dimukradiyya suke yi inda suke bukatar shugaba Buhari ya bayyana nawa ya kashe wajen duba lafiyar tasa yayin da yake kasar Ingila. Cikin wadanda suke bukatar sanin kudin da aka kashe wajen duba lafiyar shugaban akwai lauya Femi Falana, da sauran kungiyoyi kamar su SERAP, inda suka ce tunda dai Buhari na takama da shi mai gaskiya ne, toh sai ya fada ma yan Najeriya nawa ya kashe.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: