Monday, 27 March 2017

Aiki na kyau! Kunji sabon farashin dala a yau?

A wani sako da bankin ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce zai fara sayar wa bankuna dala akan Naira 357 inda su kuma bankunan kasar za su fara sayar wa ga mutane kan Naira 360.

Babban bankin yana shiga kasuwar kudaden kasashen wajen ne domin rage gibin da ke tsakaninta da ta bayan fage.

A watan da ya wuce dai kasuwar bayan fagen na sayar da dala kan N520 bayan babban bankin Najeriya ya rage darajar naira zuwa 375 ga dala daya. An sayar da dala N315 a hukumance a ranar Litinin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: