Monday, 27 March 2017

Yadda Wata Dalibar Jami'a Ta Kashe Kanta Saboda Ta Fadi Jarabawa

A cewar wani rahoto da ya iso mana, wata dalibar jami’ar kimmiya na Moddibo Adama wato Moddibo Adama University of Technology (MAUTECH) dake Yola ta kashe kanta bayan ta gano cewa ta fadi a darusa guda 9 da ta dauka.
Dalibar ta jami’ar kimiyya dake Yola, jihar Adamawa ta kashe kanta ne ta hanyar shan maganin kwari a dakunan kwanan dalibai na Oba Adetona dake jami’ar sakamakon rashin kokari da batayi a jarabawar ta.

A cewar bayanai da aka tattara, wacce abun ya faru a kanta ta kasance daliba a sashin makarantar koyar kimiyyar labarai wato School of Management and Informatin Technology (SMIT). An bayyana cewa ta kashe kanta ne bayan ta gano cewa ta fadin a jarabawar ta guda 9 na zagon farko a jami’ar.


An samu labarin cewa har yanzu hukumar makarantar bata yi wani jawabi a kan al’amarin ba. A wani al'amari makamancin haka,wani dalibin makaranta ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan budurwar sa ta kawo karshen soyayyar su.

An bayyana cewa matashin da aka karya ma zuciya ya sami wani wasika daga budurwar sa wacce ta yanke shawarar kawo karshen soyayyar su. Wannan hukunci da ta yanke ya sa shi kashe kansa a take.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: