Friday, 31 March 2017

Ya Kashe Kansa Saboda Rashin Biyansa Albashi

A safiyar jiya Alhamis ne aka samu gawar wani mutum mai shekaru 42 a rataye a jikin igiya a gidan sa da ke Yenagoa a jahar Bayelsa.
Mutumin mai suna Gbemede Kitchen ma’aikaci ne a karamar hukumar Ekeremo da ke jahar wanda sun shafe fiye da watanni 6 ba tare da an biya su albashi ba.


An ji kururuwa daga gidan mutumin bayan da ‘yayan sa guda 7 suka samu gawar baban na su a rataye a wata igiya da ya hada da zanin gado.
Wakilin gidan ya fadi yadda mutumin ya dinga kiran matar sa a waya a daren ranar a lokacin da suke wajen cajin waya. Ya ce da alamu matar ba ta nan, amma ‘yayan sa suna nan a lokacin.
Ya ce ya yi matukar mamakin faruwa wannan al’amari domin kuwa mutumin bai taba fada masa cewa ya na cikin wata damuwa ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: