Friday, 24 March 2017

Shugaba Buhari Ya Nada Sabbin Mukamai (Karanta)

Shugaba Muhammadu Buhari nada sababbin shugabanni da Darektocin Bankin manoma na kasar da ake kira BOA. Ma’ikatar noma da raya karkara ce dai ta bayyana wannan nadi da aka yi a yau Alhamis dinnan.
Lere Adams-Blessing Mataimakiyar Darektan yada labarai na Ma’aikatar noma ta fitar da wani jawabi inda take bayyama cewa shugaba Buhari ya nada Mohammed Kabiru a matsayin shugaban bankin noma na rikon kwarya.

An dai kuma nada sababbin Darektoci na bangarorin da ake da su. Darektocin dai su ne dai; Dr. Okenwa Gabriel, Aweh Owoicho da kuma Bode Abikoye. A jawabin dai ake cewa nadin zai taimaka wajen samun kudi domin harkar noma.

Da safiyar yau kuma ‘Yan kasuwa masu canjin kudi su ka fara kokawa da lamarin yayin da darajar Dala ya kara yin kasa. Idan ba ayi sa’a ba ma dai abubuwan na iya kara tabarbare masu nan gaba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: