Sunday, 2 April 2017

Idan Kaji Abinda Wani Shugaban Makaranta Yayi Sai Kayi Kuka (Karanta)

Babban kotun tarayya da ke Kano ta yankewa wani shugaban makaranta watau Hedimasta hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bayan an same sa da laifin kwanciya da kananan yara ‘yan makarantar har 2. Bayan nan kuma wannan mutumi zai biya N50, 000 ga iyalan kowane yarinya sannan kuma zai bada N50,000 ga hukuma a dalilin wannan mummunan laifi da ya aikata. Daga nan kuma zai zarce gidan kurkuku na tsawon lokaci ba tare da wani sassauci ba.
Wannan Hedimasta na Makarantar De Emirates Academy da ke Kano kamar yadda Arewarmu.com ke samun rahoto yayi lalata ne da yaran masu shekaru 6 zuwa 7 a Ofishin sa. Wannan mutum dai mai zaune a Unguwar Kabuga ya saba dokar final kwad sashe na 285 na Jihar Kano don haka zai sha dauri ba tare da daga kafa ba Inji Alkali Nasiru Saminu. Kwanaki a Kano Kotun majistare da ke Sakatariyar Audu Bako ta bada umarni a jefa wasu mutane 2 cikin kurkuku a dalilin sha’awar maza da su ke da shin a tsawon shekaru 14.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: