Sunday, 16 April 2017

Yadda Akayi Kokarin A Kashe Shugaban Kasa A Baya

Wani tsohon Kanal na Soja ya bayyana irin yadda aka yi yunkurin kashe Olusegun Obasanjo a shekarar 1998. Kanal Olusegun Oloruntoba yana cikin wadanda ba su yarda da soke zaben Abiola ba har ta kai aka jefa sa gidan yari. Takwaran tsohon shugaban kasar Kanal Olusegun Oloruntoba yace an yi kokarin kashe Obasanjo da wasu Sojoji da aka saki a 1998. Kanal din mai ritaya yace an yi yunkurin tada jirgin saman ne ya watse kowa ya mutu.
NAIJ.com na samun wannan labari ne ta wata hira da aka yi da tsohon Sojan a wata Jarida. An dai daure Janar Obasanjo da wasu manyan Sojoji a lokacin Marigayi Janar Sani Abacha, daga baya kuma Obasanjo ya zama shugaban kasa. A wannan makon aka yi kokari kashe wani Sanatan Jihar Kogi mai suna Dino Melaye. Sai dai har yanzu Jami’an tsaro ba su yi magana ba game da lamarin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: