Monday, 8 May 2017

Matsalolin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance Su – Mal. Sa’idu Kankia

– Tambaya
Matambayi: Don Allah mallam menene yake kawo matsaloli tsakanin kishiyoyi, saboda ina son na kara aure?
– Amsa
Mallam: To malam Kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A’isha tana cewa: “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi S.A.W yana ambatonta” Bukhari 1388 Kishi mai tsafta, shi ne: kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, za mu iya mayar da abubuwan da suke kawo kishi mara tsafta zuwa abubuwa guda hudu, wadanda in har da za su warwaru, to da ka ji dadin zama da matanka, saboda za su zama kamar ‘yan biyu:
1. JAHILCI: Ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar : rage yawan zawarawa da ‘yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi s.a.w., domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu.
2. MUMMUNAN ZATO: Yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima. Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba’a samu matsala ba.
3. RASHIN ADALCI DAGA WAJEN NAMIJI: Yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba. Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne: babu yadda za’a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi S.A.W ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A’isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan kirdadi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne : rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.
4. MUNAFUKAI MASU CECE-KUCE: Idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.
IDAN HAR WADANNAN MATSALOLIN ZA SU WARWARE, INA GANIN ZA A SAMU KISHI MAI TSAFTA.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: