Wednesday, 9 August 2017

Majalisa tayi magana Akan Murabus Na Shugaba Buhari, Kunji Abinda Suka yanke

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi magana a game da rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma masu kira Shugaban yayi murabus.
Wasu na ta kira Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulkin Kasar nan a dalilin rashin lafiyar da yake ta fama da ita. Majalisar tace babu wata doka kasa da Shugaba Buhari ya saba don kuwa ya bar Mukaddashi.
Majalisar Dattawa tace rashin lafiyar Shugaban kasar ba ta bar wani gibi ba don kuwa Farfesa Yemi Osinbajo ya maye gurbin na sa da kyau. Majalisar tace masu wannan kira neman suna kurum su ke yi da hayaniyar banza da wofi.

Mai magana da bakin Majalisar Dr. Aliyu Sabi Abdullahi yace 'Yan Najeriya su cigaba da yi wa Shugaba Buhari addua ne a halin yanzu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: