Friday, 11 August 2017

Tashin Hankali: Kumji Abinda Wani Magidanci Yayiwa 'Ya'yansa 4 Saboda Talauci

Galibin yan Najeriya dai suna fuskantar yanayi mai wahala bisa dalilin halin matsin tattalin arziki da kasan ta tsinci kanta tun bayan karyewar darajar kudin man fetur a kasuwannin duniya. Duk da kokarin gwamnati domin sassauta lamarin, wasu mutane dai sun kasa daure wa.

A dalilin hakan ne wani magidanci ya zubar da yayan sa guda 4 a garin Agege dake Legas bayan ya basu takarda dauke da rubutun kira ga karamar hukumar Agege ta kula da su domin ba zai iya ciyar dasu ba saboda halin matsin tattalin arziki.

Magidancin ya bayyana a cikin takardar cewa, mahifiyar yaran ce ta fara tserewa ta barshi da yaran.
Shugaban karamar hukumar Agege, Ganiyu Kola Egunjobi ya mika yaran ga ofishin yan sanda domin zurfa fa binciken gano iyayen su.

Shugaban karamar hukumar ya nuna damuwar sa da faruwar hakan tare da mamakin yadda iyaye zasu aikata haka ga yayan da suka haifa sannan ya roki yansanda da su kula da su kafin a nemo iyayen su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: