Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta yi ram da wani mutumi mai shekaru 45 da aka ambata da suna Dantani a bisa zargin aikata fyade ga wani yaro mai shekaru 9 wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Al’amarin ya afku ne a garin Zauro dake jihar ta Kebbi.
Kwamishinan yan sanda na jihar, Ibrahim M. Kabiru, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a jiya, Alhamis 10 ga watan Agusta.
A cewar sa sun damke mutumin ne bayan sun samu labarin cewa ya yi luwadi da wani yaro, mai suna Ibrahim Muhammad Dangi dan shekara 9 a dumiya, wanda hakan ya haddasa mutuwar shi.
Kwamishinan ya ce za su gurfanar da shi a gaban kotu a bisa tuhumar kisa.
A gefe guda, Kwamishinan ya ce sun kuma kama wasu maza biyu Ibrahim da Yohana a bisa zargin yi wa yara mata masu shekaru 10 da 12 fyade.
Friday, 11 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: