- Budurwar mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir har ma ta bayyana tsare-tsaren guda 9 da ta tanadar ma mutanen yankin ta idan har sun zabe ta
A halin yanzu da yan Najeriya ke shirye-shiryen fuskantar babban zaben shekarar 2019, matasa da dama na nuna sha'awarsu ta tsayawa takara a zaben.
Wannan ya biyo bayan kudirin rage shekaru na takara da Majalissar Najeriya ta rattafa hannu a kwanakin baya wadda ya baiwa matasa masu kananan shekaru damar fitowa takarar.
Wata budurwa mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir ta bayyana sha'awar ta na tsayawa takarar kujerar Sanata a yankin Bauchi ta kudu a zaben 2019 mai zuwa.
Bayan bayyana sha'awar nata ta shafin sada zumunta na Istagram, Ziyaatulhaqq ta zayyana abubuwan da zata yima al'ummar mazabar ta kamar haka:
Mazabar Bauchi ta Kudu ku fito ku zabi Ziyaatulhaqq Uman Tahir
1) Ilimi kyauta mun mun dauke wa iyayen ku
2) Zamu dauke wa iyayen yara mata kayan daki
3) Iyaye mata za'a ware masu albashin N100,000 duk wata ladan tarbiyar da suk wa yaran mu
4) Zamu hanna 'yan mata talle
5) Duk wanda yayi fyade za'ayi masa sabuwar kaciya sannan a daure shi gidan yari har tsawon shekaru 25
6) Zamu aurar da zaurawa da mutunci
7) Zamu tallafwa marayu har karshen rayuwarsu
8) Zamu gyara yankin Bauchi ta Kudu
9) Zamu kauda talauci da handama, rashin ilimi da babakere.
Ko ya wannan Al'amari zaikaya?
Tuesday, 31 July 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: