- Yace daga yanzu ba shi-ba-su, sakamakon wani sabanin da suka samu
- Ya bar mutum daya ne kacal kawai daga cikin yaran na sa wanda ake cewa Adamu Usher.
Kamar dai yadda muke samu daga majiyoyin mu rahotanni daga jihar Kaduna dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya inda ke zaman tamkar babban gari na biyu da ya tara masu sana'ar fim bayan Kano sun nuna cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa din nan kuma mawaki watau Adam A. Zango ya kori yaransa baki daya.
Mun samu cewa jarumin haka zalika cikin fushi ya kori dukkan abokan sa da ke tarayya da shi inda ya bayyana cewa daga yanzu ba shi ba su sakamakon wani sabanin da suka samu.
bayanan da muke samu daga wasu na kusa da jarumin na nuni ne da cewa ya bar mutum daya ne kacal kawai daga cikin yaran na sa wanda ake cewa Adamu Usher.
Har zuwa yanzu Zangon bai bayyana Abinda yasa yasalami yaransa ba.
Da muka kara zurfafa bincike, mun samu cewa babban dalilin da ya sa shahararren mawakin ya yanke wannan danyen hukuncin shine saboda a cewar ta sa yaran nasa ba su kare mashi mutuncin sa suna bari ana zagin sa duk da cewa yana biya musu bukatunsu daidai gwargwado.
Tuesday, 31 July 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: