Wednesday, 1 August 2018

Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Kano ya fita daga APC

Labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu na nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP.


Mataimakin gwamnan ya koma jam'iyyar PDP ne da yammacin yau Laraba, 1 ga watan Agusta 2018. Farfesa Hafiz ya dau wannan mataki ne bayan ya kawo kukan cewa wasu na kokarin daukan ransa.
Bayan wannan kuka, gwamnati ta kara masa jami'an tsaro domin karesa daga abinda yake tsoro.

wannan rahoto ne daga bakin jam'iyyar PDP inda ta saki jawabi tace: " Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya fita daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC), zuwa jam'iyyar PDP".

kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC, zuwa Peoples Democratic PArty PDP da ranan yau Laraba, 1 ga watan Agusta 2018.


Gwamnan ya bayyana wannan ne a wata hira manema labarai a gidan gwamnatin jihar Sokoto.
Ya yi wannan sanarwa ne cikin daruruwan magoya bayansa da suka yi dandazo a gidan gwamnatin jihar domin nuna goyon bayansu gareshi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: