Wednesday, 29 August 2018

Babbar magana 'An hana Kwankwaso taro a Eagles Square'



Wani jigo a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Rabiu Musa Kwanwaso, Kwamred Aminu Abdussalam, ya yi ikirarin cewa hukumomi sun hana tsohon gwamnan jihar Kano din taron siyasa a wurare biyu a Abuja.

Aminu Abdussalam ya shaida wa BBC cewa an hana su taron siyasar ne mako guda bayan da suka nemi yin amfani da dandalin Eagle Square har ma suka biya kudin hayar wajen.

Ya ce sun kuma sun nemi filin taro na Old Parade Ground a birnin Abuja, amma shi ma aka hana su, kamar yadda ya bayyana.

Kwamred Aminu ya ce tuni suka biya kudin kama wajen, kuma suka samu amincewar masu kula da filin na Eagle Square.

Sai dai ya ce 'yan sa'o'i kadan gabanin taron wanda za a yi a ranar Laraba, sai suka samu wasika daga kamfanin da ke kula da filin, inda aka ce musu ba za su iya yin amfani da wajen ba, a cewarsa.

To sai dai mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya ce babu hannun gwamnati wajen hana Kwankwaso amfani da filin.
Dan siyasar ya bayyana wannan mataki a matsayin wani yunkuri na murkushe 'yan hamayya da kuma tursasa musu.

Ya kara da cewa hakan na nuna yadda gwamnatin Buhari "ke tsoron Kwankwaso."

Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa ba gwamnati ce take tafiyar da filin na Eagle Square ba, kuma ko APC ce za ta yi taro sai ta nemi izini daga wajen masu kula da shi.

Ya kara da cewa babu kanshin gaskiya a zargin cewa gwamnati tana tsoron Kwankwaso.
A yanzu dai Kwankwaso zai yi taron kaddamar da takararsa ne a wani otel a Abuja, kamar yadda wani na kusa da shi ya shida wa BBC.

A watan Yuli ne Kwankwaso da wasu jiga-jigan APC suka fice daga jam'iyyar APC, inda suka koma tsohuwar jam'iyyarsu ta PDP.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai yana son ya sake tsayawa takarar shugaban kasa domin neman wa'adi na biyu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: