Gwamnatin tarayya ta dauki matakin rage cinkoso a gidajen yarin kasa
- Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti da aka dorawa alhakin rage cinkoso a gidajen yarin kasar
- Kwamitin mai mambobi 11 za tayi aiki ne karkashin jagorancin ministan shari'a,
Abubakar Malami
- Kwamitin za ta zagaya dukkan gidajen yarin Najeriya domin tantance wadanda suka cancanci afuwa
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya kaddamar da kwamiti na musamman domin bawa shugaban kasa shawara a kan afuwa da ragge cinkoso a gidan yarin da ke jihohin Najeriya (PACPM).
Ya kara da cewa wasu daga cikin ayyukan kwamitin sun hada da yin afuwa ga fursunonin da tsaffin da suka cancanci afuwar da kuma tabbatar da rage cinkoso a gidajen yarin da ke jihohin Najeriya baki daya.
Mustapha wanda ya samu wakilcin Ministan Shari'a na kasa Abubakar Malami, ya ce an kafa kwamitin ne domin taimakawa shugaba Muhammadu Buhari wajen gudanar da wasu ayyukansa kamar yadda doka ta tanada.
Kazalika, ya jadada cewa aikin da ke gaban kwamitin babban aiki ne kuma ya shawarci su da su fara ziyartar gidajen yari da ke jihohin Najeriya don gane wa idanunsu halin da suke ciki.
Sufeta Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris ta bakin wakilinsa Mr Shehu Lawal ya ce aikin kwamitin shine tabbatar da rage cinkoso a gidajen yarin Najeriya.
"Zamu bawa wannan aikin muhimmancin da ya kamata kuma zamu tabbatar anyi biyaya ga dokan kasa. Ba kuma zamu bata lokaci ba wajen gudanar da ayyukanmu saboda mu kammala a lokacin da aka dauka mana, " inji Sufetan 'yan sanda.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa kwamitin na da mambobi 11 kuma an basu wa'addin shekaru hudu domin kammala aikinsu karkashin jagorancin Ministan Shari'a Abubakar Malami.
0 comments: