Tuesday, 28 August 2018

Shin Kwankwaso zai iya shugabancin Nigeria?



Kwankwaso ya nemi PDP ta tsayar da shi takarar shugaban Nigeria

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce zai nemi jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan ya gana da mutane da dama.

"Bayan na yi gagganawa, na dauki matakin neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyarmu ta the People's Democratic Party," in ji dan majalisar.

A watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da wasu 'yan majalisar dattawa da ta wakilai suka fice daga jam'iyyar APC mai mulki suka koma PDP.

Sun bayyana cewa APC ba ta yi musu adalci ba duk da fafutukar da suka yi wajen ganin ta yi nasarar cinye zaben shugaban a 2015

Sai dai shugabannin APC da ma Shugaban kasar Muhammadu Buharu sun ce 'yan majalisar sun yi gajen hakuri, suna mai cewa fitar su daga jam'iyyar ba zai hana ta cin zaben 2019 ba.

Sanata Kwankwaso - wanda sau biyu yana zama gwamnan jihar Kano - zai fafata da jiga-jigan 'yan siyasa da ke neman PDP ta sayar da su takara a zaben 2019.

Cikin mutanen da ke son jam'iyyar ta ba su damar yin takarar shugabancin kasar har da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, da takwaransa na jihar Kaduna, Ahmed Makarfi da tsohon ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki da kuma takwaransa na Ilimi, Ibrahim Shekarau.

Da alama duk wanda PDP ta tsayar a zaben 2019 zai fafata da Shugaba Buhari, wanda masu sharhi a fannin siyasa ke ganin shi APC za ta tsayar a zaben.

Da ma dai Shugaba Buhari ya ayyana sha'awarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019.

Wasu dai na ganin shugaban kasar ya taka rawar a-zo-a-gani wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya don haka suke ganin ya cancanci sake cin zabe.

Sai dai wasu na ganin shugaban kasar ya sake jefa ta cikin mawuyacin halin tattalin arziki da rashin tsaro da makamantansu, suna masu cewa ya kamata a samu wanda zai maye gurbinsa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: