Ko menene Hukuncin matar Auren da take Facebook da Sauran kafar sadarwa ta zamani?, ga Ali Isah Pantami: da Amsar wannan tambaya
Shugaban hukumar kula da ci gaban fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Dokta Isa Ali Pantami ya ce ya halatta miji ya bar matarsa ta shiga shafukan sada zumunta, idan ba za ta saba wa dokokin addini ba.
Ya shaida wa BBC haka ne a wata tattaunawa ta musamman ranar Talata, inda ya ce miji na iya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter da Instagram da Whatsapp da makamantansu "idan har za ta saba wasu hakkokin addinin musulunci."
Hakazalika ya kuma ce idan har a ka bi hanyoyin da suka dace, amfani da shafukan sada zumunta na iya shigar da mutum aljanna.
'Sadar da zumunta wajibi ne a addinin Musulunci'Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar.
"Idan dai a manufofi na alheri ne, bai dace miji ya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta ba," in ji shi.
Har ila yau ya ce bai kamata matar aure ta rika abokanta da mutanen da ba su dace ba a shafukan sada zumunta.
"Ta rika abokanta da kawayenta da suka yi karatu tare, ta tarbi abokanta da yayyanta da kannenta da kuma sauran 'yan uwanta na jini," kamar yadda ya ce.
0 comments: