Dan sanda ya kashe direban mota kan cin hancin N50
- Jami'in dan sanda ya harbe wani direban mota har lahira
- Anyi zargin cewa hakan ya faru ne bayan bireban yaki ba da cin hancin N50
- Lamarin ya afku na a wani kauye dake jihar Taraba
An zargi wani jami’in dan sanda da harbe wani direban motar bus, Mohammed Dajji, har lahira saboda yaki ba da cin hancin N50.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a jihar Taraba a ranar Juma’a, 31 ga watan Agusta.
Wani idon shaida da yayi magana kan sharadin boye sunasa yace jami’in dan sandan ya harbi direban a tashar bincike dake kauyen Maisamari a Nguroe saboda yaki bashi cin hanci N50.
Fusatattun mazauna yankin da abun ya faru a idanunsu sun far ma jami’in dan sandan.
Yan sanda sun kama wani jami’in kwastam kan laifin harbin wani mai mota a tashar Iya-Afin Badagry a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.
Majiyoyin yan sanda sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Badagry cewa jami’in kwastam din wanda aka boye sunansa ya harbi wani mutum a kafadarsa na dama saboda yaki tsayawa a bincike shi.
A cewar majiya, mai motan wanda ke fitowa daga Seme Border, yaki tsayawa a inda ake duba motoci don haka sai jami’in ya bude masa wuta inda abun ya same shi a kafadarsa na dama.
0 comments: