Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa , Farfesa Yemi Osinbajo, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed, da gwamnoni sun halarci taro da shugabannin APC na kasa a Abuja.
Jam’iyyar tayi mahawara a kan hanyar da zata yi amfani da ita wurin tsarin fitar da ‘yan takara a zabukan shekarar 2019.
Ga wasu abubuwa 10 da shugaba Buhari ya fada a wurin taron:
1. Ina yiwa kowa maraba da zuwa wannan taro na kwamitin zartarwa na farko a jam’iyyar APC tun bayan zaben sabin shugabanni
2. A yayin da zabukan shekarar 2019 ke kara matsowa, akwai aiki a gaban kwamitin zartarwa na fito da tsare-tsaren yadda jam’iyyar APC zata tunkare su.
3 . Mun hadu ne, yau, a nan domin fara shirye-shiryen yadda zamu yi nasara a zabukan shekarar 2019 domin cigaba da yiwa jama’ar Najeriya aiyukan da muka fara.
4. Ina yiwa shugabancin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Adams Oshimhole murnar nuna kwarin gwuiwar cigaba da gudanar da aiyukansu ba tare da barin guguwar canjin sheka ta girgiza su ba.
5. Mun yi kokarin yin sulhu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da suka fita amma duk da haka sun bar jama’ar saboda sun dade da yanke shawarar yin hakan.
DUBA WA
6. Burin jam’iyyar APC shine samar da shugabanci da shugabanni na nagari da zasu inganta rayuwar jama’a da kare rayuwar su da dukiyoyinsu.
7. Zamu cika dukkan alkawuran da muka daukarwa jama’a. Mun cika wasu, kuma zamu cigaba da cigaba shimfida aiyukan da zasu faranta zukatan jama’a da gina kasa.
8. A yayin da muke tunkarar zabukan fitar da gwani na cikin gida, ina kira ga shugabannin jam’iyya da su gudanar da sahihan zabukan cikin gida.
9. Zabukan mu na cikin gida ya kamata su kasance sun bi ka’ida da dokokin jam’iyyar APC da kuma na Najeriya.
10. Yanzu ne lokacin da muke bukatar hadin kai da zaman lafiya a jam’iyyar mu domin ciyar da jam’iyyar mu gaba. Dole mu bawa kwamitin zartarwa na jma’iyyar mu goyon baya domin ciyar da jam’iyyar mu gaba.
0 comments: