Thursday, 30 August 2018

An yi wa Kwankwasiyya tawaye a Kano

Magoya bayan Kwankwasiyya sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a daidai lokacin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar takararsa ta shugabancin kasar a Abuja.

Dubban matuka kekunan a-daidaita-sahu da ke ikirarin cewa mabiya akidarsa ta kwankwaisiyya ne su kai wannan sauyi zuwa bangaren Gandujiyya mai mulki.

Jami`an gwamnatin jihar Kano ne suka karbe su, a wajen wani biki na musamman da aka gudanar a Kano


Ana dai zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce ta shirya bikin domin dauke hankalin jama`a daga bikin da tsohon gwamnan ya shirya a Abuja, amma ta musanta.

Shugaban jam`iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abas shi ne ya jagoranci bikin karbarsu, wadanda suka yi ikirarin cewa sun kai akalla mutum dubu biyar.

Shugaban `yan adaidaita sahun, Mallam Usama Haruna Dala ya ce rashin kyautatawa ne ya tilasta musu kaurace wa gidan kwankwasiyya.

Sai dai wasu na zargin cewa bikin karbar masu sauya shekar wata dabara ce ta kau da hankalin jama`a daga bikin da tsohon gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso ya shirya a Abuja, ganin yadda ya zo rana daya da nasa bikin.

Amma kwamishinan watsa labaran jihar Kano, Mallam Muhammad Garba ya musanta.

Wannan sauya sheka da `yan a daidaita sahu suka yi dai ba karamin kamu ba ne a wajen jiga-jigan gwamnatin APC a jihar Kano kamar yadda Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso kwamishinan raya karkara na jihar Kano ya bayyana sun gama tatike kwankwasiyya saura jagoranta:

An dade da raba-gari tsakanin gwamna Ganduje da senata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, amma adawar ta kara tsami bayan ficewar Kwankwason daga APC zuwa jam`iyyar PDP.

Kuma mabiya Gandujiyya da dama na kallon wannan neman takarar shugabancin kasar da Kwankwason ke yi a matsayin cin fuska ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin Najeriyar bai haramta masa yin haka ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: