Thursday, 30 August 2018

2019: Wasu sanatoci sunyi barazanar barin APC

Wasu sanatoci sunyi barazanar barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan har jam’iyyar taki daukar matakin yin zaben fidda gwani kai tsaye don zabukan 2019, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Majiyarmu ta tattaro cewa wasu yan majalisa sunyi gargadin cewa jam’iyyar zata sake fuskantar sauya sheka na baki daya idan har taki bin wannan tsari na gudanar da zaben fidda gwani.

Sun yi zargin cewa wasu gwamnoni na matsawa shugaban jam’iyyar lamba kan cewa yayi amfani da akasin haka ta hanyar zaben dan takara ba tare da zaben fidda gwani ba a 2019.


Sanatocin sunce idan har jam’iyyar tayi yadda ta saba wato zabar yan takara kai tsaye toh babu shakka zata sake asarar mambobinta da dama.


A ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta ne jam’iyyar APC zata gudanar da taron masu ruwa da tsaki karo na farko tun bayan barin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki jam’iyyar.

Ana sanya ran cewa zasu tatatuna akan yadda zaben 2019 zata kasance tare da irin shirye-shiryen da zasu yi mata.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: