Thursday, 30 August 2018

'Yan luwadi za su ji dadi a mulki na - inji wani dan takarar shugaban kasar Najeriya

Kamar dai kasashe da dama a nahiyar Afrika, lamarin nan na tabe dake tattare da halayyar luwadi da madigo na cigaba da fuskantar kyama daga al'umma da ma hukumomin gwamnatoci a kowane mataki a tarayyar Najeriya.

Sai dai hakan na nema ya fara sauyawa bayan da wani dan takarar shugaban kasa a tutar jam'iyyar adawa ta PDP kuma tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke ya bayyana cewa shi zai sakar masu mara suyi fitsari idan har ya zama shugaban kasa.

Majiyarmu ta samu cewa Mista Duke ya bayyana wannan ra'ayin nasa ne a yayin da yake ansa tambayoyi a cikin wani shiri na musamman da ake gabatarwa a wata tasa ta tauraron dan adam mai suna 'On The Couch' a turance.

Mista Duke a cikin firar ya bayyana cewa shi bai ma ga dalilin da zai sa yadda wani ko wata suka ga damar tafiyar da rayuwar su zai tadawa wasu hankali ba musamman ma tunda basu shiga rayuwar kowa ba.

A wani labarin kuma, Babban Limamin masallacin Juma'a na unguwar Tudun Murtala dake a garin Kano, Sheikh Abdullahi Sale Pakistan ya hadu da fushin hukuma bayan da wata babbar kotun jihar ta umurci ya mayar da wasu kudaden da ya ansa na masallacin da ya karba.

Kudin dai kamar yadda muka samu sun kai adadin Naira dubu dari tara sannan kuma ya karbe su ne da sunan bashi kusan shekaru biyu kenan da suka gabata.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: