A jiya, Talata, ne Theresa May, firaministar kasar Ingila ta ce Najeriya ce yanzu haka a sahun gaba a yawan talakawa a duniya.
Da take Magana jiya, Talata, a birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu, Theresa May ta bayyana cewar nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan mutanen da rigingimu suka raba da muhallinsu.
Har ila yau ta kara da cewa nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan talakawa a duniya, tare da bayyana cewar a kall mutane kimanin miliyan 87 ne ke fama da matsanancin talauci a Najeriya.
“Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa, amma duk da haka akwai mutane miliyan 87 na rayuwa a kasa da dalar Amurka $1 a kowacce rana, hakan ya saka kasar a gaba wajen yawan talakawa a duniya,” a cewar Firaministar ta kasar Ingila.
Ko a watan Yuni said a wata cibiyar Turai, Brookings Institution, ta bayyana cewar Najeriya ta doke kasar Indiya a yawan talakawa a duniya.
A wancan lokacin, gwamnatin Najeriya ta bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da rahoton saboda an tattara alkaluman da aka yi amfani da su ne lokacin da kasar ke cikin halin matsin tattalin arziki.
Theresa May ta bayyana cewar akwai bukatar samar da aiki ga mutane 50,000 kullum a Afrika har zuwa shekarar 2035 domin shawo kan matsalar talauci a nahiyar.

0 comments: