Wani matashi ne bai da lafiya , ciwo yaki ci-ya-ki cinyewa sai wani mai magani ya ce masu bazai warke ba har sai an hura wuta sannan sai shi matashin su shiga shi da daya daga cikin wa’yanda ya fi so su kwana amma ba abinda zai same su sannan zai warke.
Ai ko haka aka yi sai aka hura wuta aka ce mahaifiyarsa ta shiga ta ce sam ba ta san da zancen ba, don ita ba ta gaji da duniya ba kawai a bar shi ya mutu,
Sai budurwarsa tace ita tana son sa, a sa su a ciki, aka hura wuta suka shiga washe gari ya warke suka fito sumul, mahaifiyarsa ta fi kowa murna.
A kan hanyarsu ta dawowa gida sai ga zomo zai wuce sai yarinyar tace tana so ya kama mata ,ya dauki abin jifa zai yi jifa kenan sai zomon ya waigo ya ce da shi, kana jifa na mahaifiyarka za ta mutu, in kuma ka fasa budurwarka zata mutu….
in kaine wanne zaka yi?,

Tsaka mai wuya kenan😂
ReplyDeleteWallahi pasawa zanyi
ReplyDelete