Thursday, 30 August 2018

Illoli 5 Da Saka Takalma Masu Tsini Ke Haifarwa Ga Lafiya

Likitoci a fadin duniya sun dade suna gargadin mata game da manya manyan illolin da sanya takalma masu tsini ke haifarwa ga lafiya da kasusuwan jikin su, amma da ya ke abu ne da ya jibanci gayu, sau da yawa sai dai a yi watsi da shi.

Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Havard da ke kasar Amurka ya nuna cewa kari a tsahon takalmi ko da da inci biyu ne ya na kara yiwuwar kamuwa da cututtukan kashi da kaso 23 cikin dari.


Ga kadan daga cikin illolin da ke tattara da sanya irin wannan takalma kamar yadda likitoci suka bayyana:

1. Haifar da cututtukan kashi

2. Lalata kashin bayan mutum

3. Haifar da matsala ga gwiwowi da gabobi da tafin kafa

4. Su na raunata jijiyoyin da ke tafiyar da jini a jikin dan adam

5. Su na hassasa yiwuwar kamuwa da cutar hawan jini da ciwon siga a lokacin tsufa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: