Thursday, 30 August 2018

Hanya Mai Sauki Da Ake Magance Fason Kafa

Fason kafa ya kan zamewa mutane karfen kafa musamman ma a lokacin sanyi, ko a yankunan da suka fi bushewa fiye da wasu.

Wannan ya na faruwa ne saboda fatar kafa ta fi ta sauran sassan jiki bushewa kuma tana bukatar kulawa ta musamman wanda yawancin lokuta ba ta samu.
Rashin kula da faso ka iya ta’azzara shi ta yadda zai iya fara jini, ko ciwo ko kuma kwayoyin cuta su shiga ciki.
Ga wata hanya mafi sauki da ake magance wannan matsala:
Ruwan Kal (Farin Vinegar ko Apple Cider Vinger)
  • Za a zuba ruwa a cikin babbar roba, sanna a zuba ruwan kal kamar 1/4 na Kofi daya
  • Sai a jika kafar a ciki na tsahon minti 10 zuwa 15
  • A yi amfani da Dutsen kaushi wajen gurje fatar da ta jiku, sai a yi amfani da farin ruwa wajen dauraye kafar.
  • Bayan a goge ta da tawul mai tsafta, sai a shafa man kwakwa, ko Zaitun ko kuma man Kadanya.
  • Za a maimata sau uku a sati.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: