YAYIN BUDE MUHIMMAN AYYUKKA A JIHAR ZAMFARA.
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Jihar Zamfara Domin bude wasu Muhimman Ayyukan A jihar ta zamfara karkashin jagorancin gwamnan jihar ta zamfara Abdul Aziz Yari A jiya Talata.
A Ziyarar ta mukaddashin shugaban kasa ya jagoranci bude Babban Asibitin A garin Bakura dake cikin jihar ta zamfara.
Sannan kuma ya jagoranci bude Gidan ruwa na fanfo na zamani mai Amfani da hasken rana wato (Soler) A garin Gamji duk A jihar zamfara.
Sannan kuma ya ziyarci sansanin yan gudun hijira inda Anan ma ya jagoranci bayar da Kayan tallafin agajin gaggawa wanda aka bai wa mutanen da Yan Ta'adda da suka rabo su daga Muhallansu wanda yake a karkashin Hukumar Kula da bayar da Agajin gaggawa ta kasa wato (Nema) duk A jihar ta Zamfara.
Daga karshe Mukaddashin Shugaban kasa ya jagoranci bude Sabuwar hanyar Bye-Pass a garin Talata Mafara, da kuma bude Babbar Makarantar firamare ta Abubakar Tunau duk A garin Talata Mafara dake cikin jihar ta Zamfara.
Wednesday, 15 August 2018
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: